News
Rikicin Masarautar Kano : Kashim Shattima Ya Ayyyana Sunusi Lamido A Matsayain Sarki Na Goma Sha Shida
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Bayan daukar lokaci anata shari’a tsakanin bangaren sarautar Sarki Muhammad Sunusi Lamido Sunusi II da Sarki Aminu Ado , mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima ya ayyyana Sarki Muhammmad Sunusi Lamido Sanusi II a matsayain Sabon sarkin na Goma sha Shida 16 a Jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mataimakin shugaban Shattima ya ayyana hakan ne a shafin sa na Facebook da X Twitter inda ya bayyana Sarki Sanusi a matsayin sarki na 16.
Tom sai dai a iya cewa lamarin yazo da rikitarwa musamman ma a shafukan sada zumunta da ake ganin yadda jam’iyyar APC akoda yaushe take ayyyana sarki Aminu Ado a matsayin halataccen sarki duk kuwa da cewa haryanzu anata fafata sharia’a a kotu tsakanin sarakunan guda biyu.
Ayyyana Sarki Muhammmad Sunusi Lamido Sunusi da mataimakin shugaban Ƙasa Kashim Shattima yasa wasu daga cikin Jama’a ke ganin Sarki Muhammmad Sunusi Lamido Sunusi a matsayin halataccen sarki tun bayan amincewa da halaccin sarautar Kano.
Yayin da rikicin Masarautar Kano ke ci gaba da kasancewa a gaban kotu, jihar ta shaidi sarautu guda biyu wato Sanusi da na 15, Aminu Ado Bayero.
Cikin rubutun daya wallkafa a shafukan sada zumanta mataimakin shugaban Ƙasar ya ce a ranar Asabar, na halarci daurin auren diyar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso.
Idan ba’amantaba jaridar Inda ranka a jiya ta rawaito cewa Kwankwaso ya aurar da diyarsa, mai suna Dr. Aishatu Kwankwaso da Fahad, dan hamshakin dan kasuwan nan mazaunin Katsina, Alhaji Dahiru Mangal.
Babban limamin Kano Farfesa Sani Zahraddeen ne ya gudanar da daurin auren a fadar mai martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II akan sadakin aure Naira Miliyan Guda.
Sai dai bayan fitar hakanne masu amfani da shafukan sada zumunta suka yi ta mahawara wanda yasanya daga baya aka gyara layii na uku dake cikin sakon tare da cire sunan sarkin.
Da yake mayar da martani, wani mai amfani da shafukan sada zumunta, Alhassan Ali Lawan ya ce, “Mun yi farin cikin karrama wannan gayyata mai girma! Muna kuma farin cikin amincewa da Sarkinmu a matsayin Sarkin Kano na 16.
Wani ma’aikacin mai suna Najeeb Sule Alfindi ya ce, “Mafi kyawun rubutun daya burge ni shi ne sakin layi na 3, inda Kashim Shattima na godewa Allah dana halacce taran daurin aure a fadar Sarkin Kano, Muhammad Sunusi na biyu.
Musa Kabir ya rubuta, “Masha Allah! Mai girma gwamna a madadin mutanen jihar Kano mun yaba da zuwan ku. Na san za ku iya hada shiyoyin goepolitical zones guda shida a kasar nan.
Sannan wani ya ce ina matukar jin dadin maganarka ta biyu wacce ta kira Sarkin Kano na 16. Malam Sunusi Lamido Sunusi shine zabinmu kuma ina yi maka addu’a wata rana ka zama jagoran wannan Al’umma
