Connect with us

News

Babbar Magana: An Sace Birkin Jirgin Sama Guda A Kano

Published

on

Babbar Magana An Sace Birkin Jirgin Sama Guda A Kano
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kotun majistret mai lamba 70 da ke jihar Kano, karkashin jagorancin mai Shari’a Faruk Ibrahim Umar, ta aike da wasu mutane gidan ajiya da gyaran hali bisa zargin su da hada baki da Sata.

Kunshin zargin da ake yi wa mutanen ya ayyana cewar, a ranar 11 ga watan 12 na shekarar da ta gabata ta 2025, wani mutum mai suna Otaru Bashir ma’aikaci a kamfanin sifirin jiragen sama na Azman, ya yi korafı cewar mai gadin kamfanin nasu ya hada baki da wasu mutane sun sace musu birkin jirgin sama guda 80.

Advertisement

Almajirai Da Ƴan Jari-bola Sun Maka Ministan Abuja a kotu

Ana dai zargin mutanen ne da sace wadannan barakun wato birkin jirgin sama guda tamanin a filin jirgin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.

Mutanen da ake zargin sun hadar da Nuhu Auwalu da Yakubu Bala da Emanuel Luka, sai kuma safiyanu Abdullahi.

Ko da aka karanta wa mutanen kunshin zargin da ake yi musu dukkaninsu sun musanta, a nan ne kotun ta aike da mutanen gidan gyaran hali tare da sanya ranar 11 ga watan gobe dan sauraron shaidu akan shari’ar.

Advertisement

DALA FM ta ruwaito cewa yayin zaman kotun an ambata cewar, binciken yan sanda ya bayyana cewar kimar kayan ya kama Naira miliyan dari da arba’in, sai dai yayin bincike an gano birkin jirgin guda uku a hannun wanda ake zargi na uku mai suna Yakubu

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *