News
Samarwa Matasa Ci Gaba Shine Babban Burin mu — Gwamnatin Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai bawa Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf shawara kan harkokin matasa da wasanni, Alhaji Sani Danja, ya bayyana cewa samar da ci gaba ga matasa shine babban burinsu.
Ya yi wannan jawabi ne yayin da ya karbi bakuncin manema Labarai a yau, inda ya jaddada cewa Gwamnatin Jihar Kano ta dukufa wajen inganta rayuwar matasa da samar da ci gaba mai dorewa, musamman a bangaren wasanni da kuma tallafawa mata.
Samarwa Matasa Ci Gaba Shine Babban Burin mu — Gwamnatin Kano
Alhaji Sani Danja ya bayyana cewa gwamnatin ta himmatu wajen yaki da dabi’un da ba su dace ba, irin su fadan daba da shaye-shaye, domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a fadin jihar.
Ya kara da cewa Jihar Kano tana zama wata cibiyar koyi ta gari, inda ake kwaikwayon kyawawan manufofinta a fadin kasa.
Gwamnatin jihar tana ci gaba da daukar matakai masu karfi wajen tabbatar da cewa matasa sun samu guraben ci gaba ta fannoni daban-daban.
