Connect with us

News

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Wata Budurwa Bayan Sun Karɓi Kuɗin Fansa Miliyan 8 A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ƴan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta.

Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta.

‎Ɓarawo Ya Mutu Sakamakon Konewa Da Wutar Lantarki Yayin Da Ya Ke Kokarin Sata A Taransifoma

Ana zargin masu garkuwa da mutane sun kai hari gidan wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Auwal, inda suka sace babbar ‘yarsa, Zainab, bayan sun karɓi kuɗi har naira miliyan takwas (₦8,000,000) daga iyalinsa.

Shaidu sun bayyana cewa maharan, kimanin su goma, sun farmaki gidan da misalin ƙarfe 1:20 na dare, inda uku daga cikinsu ke da bindigogi, sauran kuma na ɗauke da makamai daban-daban.

Lamarin ya haifar da firgici a cikin al’umma, inda mazauna yankin ke kira ga mahukunta da su ɗauki matakan magance matsalar rashin tsaro da ke ƙaruwa a yankin.

Advertisement

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda mai magana da yawun ta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa an fara bincike don cafke waɗanda suka aikata lai

fin.”

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending