News
An Bukaci Shugaban Yan’ Sanda Na Ƙasa IGP Kayode Egbetokun Ya’yi Ritaya Daga Mukaminsa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani babban Lauya Mai mukamin (San) a Nageriya, Ayotunde Oguntleye ya bukaci shugaban Yan Sanda na Ƙasa (IGP) Kayede Egbetokun yayi ya’yi ritaya daga mukaminsa.
Lauyan ya ce shekarun da doka ta ta debarwa IGP na aiki sun wuce shekara 60, adan haka ya kamata ace Egbetokun ya yi ritaya kamar Yadda Channel ta rawaito.
Shima tsohon dan takarar shugabancin Ƙasa a Jam’iyyar African Action Congress (AAC) Omowole Sowore ya ce aikin da IGP a yanzu ya keyi ya saba da dokar tsarin mulkin Ƙasa kamar Yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.
Dokar squashing ta tsarin aikin gwamnati ta ce muddin har mutum ya Shekara 60 yana aiki koda shekarun aiki Basu cimmasa ba ya zama dole ma’aikaci ko waye ya ajiye aikinsa a cewar Lauyan.
Rahotanni sun tabbatar da cewar an nada Egbetokun a matsayin IGP a watan Yuni 2023 kuma ya kasance har yanzu shine Shugaban da ya’ke jagorantar rundunar ‘yan sanda ta kasa.
Egbetokun wanda aka haifa a ranar 4 ga Satumbar 1964 ya kamata ace yayi Ritaya daga aiki tun a watan Satumbar Shekara 2024 a cewar Lauyan.
Dokar tsarin Mulki Ƙasa ta ce duk ma’aikacin gwamnati da yakai shekaru 60 lokaci ne daya kamata ace ya ajiye mukaminsa koda ace bai cike shekarun 35 yana aiki kamar yadda dokar ‘yan sanda ta 2020 ta ce.
