News
Jami’an Hukumar NDLEA Sun Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta NDLEA reshen jihar Kano sun gargadi iyaye kan yaɗuwar wasu alewa da cicin da ake zargin suna ɗauke da sinadarai masu sa maye.
Wannan gargadi ya fito ne ta cikin wani bidiyo da kakakin hukumar, ASN Sadiq Maigatari, ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana damuwar hukumar kan yawaitar wadannan kayan zaƙi da ake sayarwa ga yara ba tare da sun san illa da ke tattare da su ba.
Maigatari ya yi bayanin cewa wasu alewoyi da suka yi kama da cakuleti na yau da kullum na iya ɗauke da sinadarai masu sa maye, kuma ana sayar da su cikin sauƙi ga yara. Saboda haka, ya buƙaci iyaye da masu kula da yara su riƙa duba sinadaran da aka haɗa da kayan zaƙi da cocin da ‘ya’yansu ke ci ko sha, domin kaucewa haɗarin shan ƙwayoyi.
“Ina so iyaye su lura da alamomin ganye ko wasu alamomi masu alaƙa da tabar wiwi da ake iya gani a jikin kwali ko murfin kayan zaƙin. Ya zama dole su kasance masu taka tsantsan domin kare ‘ya’yansu daga shan irin waɗannan abubuwa,” in ji Maigatari.
Hukumar NDLEA ta kuma yi kira ga al’umma da su taimaka da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen dakile yaduwar wadannan kayayyaki a cikin al’umma.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
