News
Jami’an Tsaro Sun Harbe Mutane 4, Tare Da Raunata Wasu 16 A Yayin Rushe Gidaje Da Kwangaye A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Jami’an tsaro sun harbe mutane hudu tare da raunata wasu 16 a yayin atisayen rushe gine-gine da gwamnatin Jihar Kano ta gudanar a Rimin Zakara, kusa da Jami’ar Bayero ta Kano, a Karamar Hukumar Ungogo.
Rusau din, wanda ya shafi gine-gine sama da 18, ya faru ne a daren Lahadi, lamarin da ya haifar da turjiya daga mazauna yankin, wadanda suka ce ba a basu isasshiyar sanarwa ba kafin rushewar.
Jami’an Hukumar NDLEA Sun Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano
Wani ganau, Malam Sunusi Dan-Baba, ya shaidawa SolaceBase cewa tawagar rusau ta iso da daddare, inda suka fara ruguza gidaje da shaguna. Ya bayyana cewa ana takaddama kan mallakar filin tsakanin Jami’ar Bayero da mazauna yankin tun sama da shekaru 20 da suka gabata.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) reshen Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa an tura jami’an tsaro don kare kadarorin gwamnati, amma mazauna yankin sun kai musu farmaki, sun raunata jami’i daya, tare da lalata motocin su.
A nata bangaren, Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsare ta Kano ta tabbatar da cewa filin na Jami’ar Bayero ne, kuma an bi duk hanyoyin doka kafin rusau din. Daraktan yada labarai na ma’aikatar, Umar Abdu Kurmawa, ya ce an bayar da sanarwa tun kafin aiwatar da rusau din, har ma an biya diyya ga wadanda abin ya shafa sama da shekaru 20 da suka wuce.
Lamarin ya haifar da cece-ku-ce a tsakanin mazauna yankin, inda suke bukatar a gudanar da bincike kan kisan mutanen da aka yi, tare da fayyace mallakar filin da ake takaddama a kai.
Duk kokarin jin ta bakin Daraktan Hulda da Jama’a na Jami’ar Bayero, Malam Lamara Garba, bai yi nasara ba, domin wayarsaa kashe take.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
