News
Yan Bindiga 23 Sun Ajiye Makamansu Bayan Wani Musayar Wuta Tsakaninsu Da Sojoji
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
A kalla Yan Bindiga su 23 ne suka ajiye makamansu bayan wata Musayar wuta da sukayi tsakaninsu da Sojoji a garin Karim Lamido ta Jihar Taraba.
Cikin wata sanarwa da shugaban tawagar ya fitar, Birgediya Kingsley Uwa, ya ce Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu bayan wani sumamen aiki da rundunar ta kaiwa Yan Bindigar.
A cewarsa , Sojojin sun sami rahotan inda Yan Bindigar suka kafa sansani wato inda suke a zaune tom daga anan ne fa Sojojin suka shirya domin tunkarar Yan bindigar.
Bayan Sojoji sun Isa gurin ne aka fara musayar wuta tsakanin bangarorin Biyu anan ne Yan Bindigar suka su 23 suka mika kansu ga Sojoji kamar yadda jaridar People Gazette ta rawaito.
Shigaban kwamandan Birgediya Uwa, ya ya ce a lokacin sumamen sojojinsu sunyi nasarar karbe makamai da dama da suka hadar da Bindigo kirar AK-47, tare da harsashai.
Haka zalika Kwamandan Birgediy ,Uwa ya bada tabbacin Inganta tsaro a Jihar Taraba da kewayenta
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
