News
Da Dumi Dumi : Gwamnan Kano Ya Naɗa Umar Faruk Ibrahim A Matsayin Sabon Sakateran Gwamnati
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Kano wato (SSG).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa jaridar Inda ranka a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce nadin Ibrahim zata fara aiki daga ranar Litinin 10 ga Fabrairu, 2025 bayen maye gurbinsa da tsohon sakataren gwamnatin Alhaji Baffa Bichi.
Haka zalika Sanarwar ta ce, an zabi Ibrahim ne bisa gogewar da yake da ita, wanda ake sa ran zai yi amfani da ita wajen inganta harkokin gwamnatin jihar Kano.
Umar Farouk Ibrahim dai ya kwashe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati , don haka ake fatan zai kawo cigaba sosai a sha’anin tafiyar da harkokin aikin gwamnati.
