News
Majalisar Wakilai Ta Umurci NCC Da Ta Rufe Shafukan Intanet Na Batsa
Majalisar Wakilan Nijeriya ta bai wa Hukumar Kula da Sadarwa ta Ƙasar, NCC umarnin a gaggauta rufe duk wasu shafukan intanet na batsa a fadin ƙasar.
A wani zama da ta yi a ranar Talata ne majalisar ta bukaci NCC da ta umarci dukkan masu samar da intanet da su taƙaita shiga irin waɗannan shafuka da gaggawa.
Wani ɗan majalisa daga jihar Katsina Dalhatu Tafoki ne ya ɗauki nauyin ƙudirin a ranar Talata a zauren majalisar.
Tafoki ya koka cewa, duk da barazanar da ake fuskanta na yaduwar batsa a duniya, Nijeriya ta kasa aiwatar da ƙwararan matakai na daƙile hanyoyin kallon batsa.
Ƙudurin ya damu sosai cewa wasu daga cikin illolin kallon abubuwan batsa sun haɗa da:
Haifar da yaudara a cikin aure wanda daga baya zai iya shafar rayuwar iyali;
Ƙaruwa zinace-zinace da karuwanci da ganin abubuwa marasa kyau na rayuwar ƙarya waɗanda za su iya haifar da munana halaye masu haɗari;
Haifar da jaraba da zamar da abin jiki da ta’azzarar istimna’i a tsakanin al’umma da kuma sauya ɗaib’u da halayen mutane a karan-kansu da a tsakanin iyalansu.
Fatan ƙudurin
An yi kira ga Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) da ta umarci masu samar da Intanet (SPs) da ke aiki a kasar da su dauki matakin toshe duk shafukan intanet din da ke dauke da abubuwan batsa;
An kuma buƙaci NCC da ta yi amfani da cikakkun ka’idojin dokar sadarwa na Nijeriya da kuma dokar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa a kan duk kamfanonin da ke samar da intanet da suka gaza bin dokar.
Sannan an umurci kwamitocin sadarwa da bin doka da oda don tabbatar da aiwatarwa da bayar da rahoto cikin makonni hudu don majalisa ta ɗauki ƙrin matakai.
