News
Rahar Da Buhari Ya Yi Wa Atiku A Kaduna Ta Haifar Da Cece-kuce

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karɓi bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a gidansa da ke Kaduna, yayin da suka yi raha mai ɗaukar hankali da ta tayar da cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Ziyarar da aka kai a ranar Juma’a, ta gudana ne da rakiyar fitattun ‘yan siyasa irin su tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal, tsohon ministan sadarwa Isa Ali Pantami da sauransu.
Ziyarar Ganduje Mai Dauke Da Abun Kunya —Daga Adnan Mukhtar
A cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ji Buhari cikin raha yana cewa, “Salamun alaikum. Ina yi muku maraba. Sannunku da gwagwarmaya,” yana mai dariya da nishaɗi yayin da yake gaisuwa da wadanda suka halarci ziyarar.
Sai dai kalmar “gwagwarmaya” da Buhari ya yi amfani da ita ta janyo cece-kuce, kasancewar bai fayyace ainihin gwagwarmayar da yake nufi ba. Masu lura da al’amura sun fassara hakan a matsayin wani harin nuni ga kokarin Atiku wajen kalubalantar jam’iyyar APC a zabuka.
A gefe guda, Atiku ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa ziyarar ta kasance ne domin gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban kasa. “A matsayina na Wazirin Adamawa, bayan sallar Sallah tare da Lamido Fombina, na kai wa shugaban kasa Buhari ziyarar gaisuwar Sallah. Mun yi dariya da raha kamar yadda muka saba,” in ji Atiku.
El-Rufai ma ya bayyana cewa ba siyasa ke tattare da wannan ziyara ba, yana mai cewa, “Bai kamata hamayyarmu ta hana mu bacci ba. Wannan ziyara ba ta siyasa ba ce, ta ‘yan uwantaka ce da nuna girmamawa.”
Dele Momodu da sauran ‘yan siyasa da suka halarci ziyarar sun bayyana cewa manufar su ita ce nuna daraja da martaba ga tsohon shugaban kasa, ba tare da la’akari da banbancin jam’iyya ba.
Wasu daga cikin manyan da suka raki Atiku sun haɗa da: Mohammed Bindow (tsohon gwamnan Adamawa), Achike Udenwa (tsohon gwamnan Imo), Gabriel Suswan (tsohon gwamnan Benuwai), Sanata Idris Umar, Mohammed Kumalia, Yahaya Abubakar, Musa Halilu da Salisu Makarfi.
Atiku dai ya fuskanci Buhari a zaben 2019 inda ya sha kaye, sannan ya fadi a karawar da ya yi da shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu a 2023. Buhari kuwa ya yi mulki daga 2015 zuwa 2023 karkashin jam’iyyar APC, wacce har yanzu ke rike da mulki a Najeriya.