Connect with us

News

Sojojin Najeriya Sun Ce Sun Kashe Ƙasurgumin Dan bindiga Gwaska Da Wasu Guda 100 A Katsina

Published

on

An yi wata musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da tawagar dan ta'adda Bello Turji

Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin guiwar rundunar sojin sama sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Gwaska tare da wasu ƴan bindiga 100 a wani gagarumin samame da suka kai a dazukan jihar Katsina.

Kwamishinan Tsaro da Lamuran Cikin Gida na jihar Katsina, Dr. Nasir Mua’zu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a. Ya bayyana cewa wannan aikin na cikin dabarun da gwamnatin jihar ke ɗauka domin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Advertisement

Wani Mutum Ya Rasa Ransa Bayan Zargin Satar Kare A Bauchi

A cewar sanarwar, hare-haren da dakarun suka kai ranar 10 ga Afrilu 2025 sun gudana ne a dazukan Mununu Bakai, Zango, Jeka Arera, Malali da Ruwan Godiya – waɗanda ke cikin ƙananan hukumomin Kankara da Faskari.

“Bisa sahihan bayanan sirri, dakarun sun kai farmaki kai tsaye kan sansanonin ɓarayin daji, inda aka hallaka Gwaska – wanda ake nema ruwa a jallo, kuma mataimaki ne ga wani shugaban ƴan bindiga da ke da alaƙa da ISWAP,” in ji Mua’zu.

Advertisement

An gano cewa Gwaska ya ƙaura daga ƙaramar hukumar Danmusa zuwa dajin Mununu kwanan nan, kafin ya gamu da ajali a harin.

Bayanai sun ƙara nuna cewa dakarun sun lalata manyan bindigogi biyu masu jigida da kuma wasu bindigogi da aka ƙera a gida. Haka kuma, an kwato makamai da dama domin hana amfani da su wajen aikata laifuka a nan gaba.

Advertisement

A wani hari dabam da aka kai da sanyin safiyar ranar Juma’a a hanyar Dutsen Wori, tsakanin Dandume da Kandamba – dakarun sun kashe ƴan bindiga shida ciki har da shugabansu. Rahotanni sun nuna cewa sauran sun tsere da raunukan harbin bindiga.

An bayyana cewa dakarun sun kwato babura bakwai yayin da wasu huɗu suka tsere cikin dajin. Wannan samame ya biyo bayan wani sahihin bayani da aka samu daga yankin Maigora/Doroyi cikin ƙaramar hukumar Faskari.

Advertisement

Kwamishinan ya ƙara da cewa waɗannan hare-hare sun kasance barazana ga ƙungiyoyin masu aikata laifi a jihar, kuma matakin zai taimaka gaya wajen dawo da zaman lafiya a yankunan da rikice-rikicen suka addaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending