News
Wani Mutum Ya Rasa Ransa Bayan Zargin Satar Kare A Bauchi
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa tana gudanar da bincike kan wani mummunan lamari da ya auku a unguwar Lushi da ke cikin garin Bauchi, inda wasu matasa suka yi wa wasu mutane biyu dukan kawo wuka bisa zargin satar kare.
Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar ɗaya daga cikin mutanen da ake zargin, mai suna Peter, yayin da ɗaya, Dokagk Danladi mai shekaru 38, ya samu munanan raunuka.
Batagari Sun Tursasa Mai Juna Biyu Ta Haihu, Sun Gudu Da Jaririn A Kano
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Laraba, 9 ga Afrilu, 2025.
A cewarsa, “Dokagk ya samu raunuka masu tsanani, ciki har da sara a kansa da aka yi masa da adda. Tuni aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) domin kula da lafiyarsa. Abokin nasa Peter kuwa, an same shi a wajen da lamarin ya faru, amma ma’aikatan lafiya sun tabbatar da mutuwarsa.”
Rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin tare da kokarin gano duk wanda ke da hannu a cikin wannan aika-aikar.
Kakakin rundunar ya kara da cewa babban jami’in ‘yan sanda da ke kula da shiyyar Yalwa (DPO) yana jagorantar tawagar bincike da ta ziyarci wurin don tattara shaidu da bayanai masu muhimmanci.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya bayyana lamarin a matsayin “ɓarna da kuma barazana ga tsarin doka da oda a ƙasar nan.” Ya kuma gargaɗi jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.
“Babu wanda ke da ikon hukunta wanda ake zargi da aikata laifi. Ya kamata a miƙa su ga hukumomin da abin ya shafa domin gudanar da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu,” in ji kwamishinan.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da bada haɗin kai ga rundunar domin tabbatar da adalci a wannan lamari.
