News
Gobara Ta Tashi A Rumbun Makamai Na Barikin Giwa A Maiduguri

Wata gobara da ta tashi a rumbun adana makamai na barikin sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ta jefa al’umma cikin fargaba.
Shaidun gani da ido sun ce karar abubuwa masu fashewa da aka ji a cikin daren Laraba ne ya tayar da hankalin jama’a a yankuna daban-daban na birnin.
Ba Wanda Zai Iya Kayar Da Tinubu A Zaben 2027 Sai Dan Arewa —Dele Momodu
Wasu rahotanni da suka fara yaduwa sun danganta gobarar da hari daga ‘yan kungiyar Boko Haram, sai dai hukumomin jihar sun karyata hakan.
Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Dakta Umar Usman Kadafur, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da zama cikin gidajensu domin gujewa hadurra.
Ya ce jami’an tsaro da na kashe gobara na kokarin shawo kan lamarin, kuma babu wani tabbaci da ke nuna cewa hari aka kai barikin.
“Bincike na ci gaba domin gano musabbabin gobarar,” in ji shi.
Har zuwa yanzu ba a samu cikakken bayani ba kan abin da ya kone ko ko akwai asarar rayuka.