News
UTME 2025: JAMB Ta Kama Mutane 40 Da Ake Zargi Da Satar Amsa
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta ce ta kama mutane fiye da 40 da ake zargi da aikata laifin satar amsa a jarabawar UTME ta bana.
Shugaban hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, inda ya ce tuni jami’an tsaro suka cafke wadanda ake zargin.
Gobara Ta Tashi A Rumbun Makamai Na Barikin Giwa A Maiduguri
Ya ce, “Mutanen na tsare a hannun jami’an tsaro, kuma da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da su domin a yanke musu hukunci bisa laifukan da ake zarginsu da su.”
Farfesa Oloyede ya bayyana cewa hukumar ta dauki matakan tsaro na musamman tun daga lokacin da ake yi wa dalibai rajista, har zuwa lokacin da suka shiga dakin rubuta jarabawar.
A bana, dalibai sama da miliyan biyu ne suka yi rajistar jarabawar UTME, yayin da a bara adadin ya kai sama da miliyan 1.9. A shekarar da ta gabata, hukumar ta kwace sakamakon jarabawar dalibai 64,000 saboda zargin satar amsa, kodayake daga bisani ta saki sakamakon wasu bayan ta tabbatar da cewa ba su da laifi.
Korafe-korafe Kan Tura Dalibai Wurare Masu Nisa
Wasu iyaye da dalibai sun koka kan yadda JAMB ke tura masu jarabawa zuwa wurare masu nisa domin rubuta jarabawar, lamarin da a wasu lokuta ke jefa rayukansu cikin hadari.
An samu rahoton hadarin mota da ya yi sanadiyar mutuwar wasu dalibai a hanyar Oyo zuwa Ogbomoso, yayin da wata yarinya ta bace daga Ajah a jihar Legas, kuma daga bisani aka same ta a Ijebu Ode, jihar Ogun.
Sai dai hukumar ta musanta zargin cewa tana tura dalibai wurare masu nisa da gangan. Ta ce a bana ta dauki matakin tura dalibai zuwa cibiyoyin da suka fi kusa da su, domin kauce wa irin wadannan matsaloli.
Me ya sa JAMB ke saka jarabawa da wuri?
Game da korafi kan saka lokacin fara jarabawa da wuri, JAMB ta ce hakan yana da dalili.
“Mun sanya cewa dalibai su isa wurin rubuta jarabawa tun karfe shida na safe, amma jarabawar ba ta fara sai da karfe takwas. Wannan na bai wa ma’aikata damar tantance dalibai da kuma shirya abubuwa yadda ya kamata,” in ji Oloyede.
Hukumar ta ce an raba daliban zuwa rukuni-rukuni domin saukaka gudanarwar jarabawar:
Rukuni na farko na fara da karfe takwas na safe,Na biyu da goma da rabi,Na uku da karfe daya na rana,Sai na hudu da karfe uku da rabi na rana.
JAMB ta bukaci duk dalibi da zai rubuta jarabawa da ya tabbatar ya isa wurin da wuri, domin kauce wa cikas da zai iya hana shi rubuta jarabawar.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
