Sports
Wasu Fusatattu Matasa Sun Kona Alkalin Wasan Ƙwallon ƙafa A Gaban Jama’a

Wasu gungun fusatattun matasa sun yi wa wani mashahurin alkalin wasan ƙwallon ƙafa dukan tsiya tare da ƙonashi da ransa a garin Bukavu da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Alkalin, Patrick Ngalamulume wanda aka fi sani da Ngalas, ya rasu yana da shekaru 36 a duniya.
Rahotanni sun ce an zarge shi da laifin sata, zargi da ba a gabatar da wata hujja a kai ba.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Talata, 6 ga watan Mayu, kuma ya tayar da hankula a yankin, inda jama’a ke bayyana damuwa kan yadda rashin tsaro da kin bin doka da oda ke ƙara kamari.
Kisan gilla da aka yi wa Ngalas ya sake nuna irin mawuyacin halin da ake ciki a gabashin ƙasar, wadda ke fama da rikice-rikice da rashin zaman lafiya tsawon shekaru.