News
Sarkin Jinkan Hausawan Afrika Ya Jajantawa Yan Kasuwar Waya Ta Farm Center Kan Gobarar Suka Yi

Sarkin Jinkan Hausawan Afrika, Ambasada Ibrahim Ali Ibrahim (Abba Alra-iwas), ya nuna cikakken tausayawa da jajantawa ga yan kasuwar waya ta Farm Centre dake Kano, sakamakon gobarar da ta afku kwanan nan a kasuwar.
A cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Sarkin ya bayyana alhinin da zuciyarsa ke ji game da wannan mummunar gobara, tare da addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya mayar musu da duk abin da suka rasa, ya kuma ba su ƙarfin guiwar sake farfado da kasuwancin su.
Sanata Barau Ya Kai Ziyara Kasuwar Waya Ta Farm Centre, Ya Ba Da Tallafi Naira Miliyan 200
Sarkin Jinkan ya yi kira mai ƙarfi ga gwamnati, shugabannin kasuwa, da al’umma baki ɗaya, da su ɗauki matakan gaggawa wajen kafa doka da tsauraran ƙa’idoji game da ajiye da amfani da na’urorin samar da wuta a cikin kasuwanni.
Wannan zai taimaka matuƙa wajen hana sake faruwar irin wannan gobara da zata iya lalata dukiyoyin al’umma.
Ya bayyana cewa, tsaron rayuka da dukiyoyi na ‘yan kasuwa wajibi ne, kuma tilas ne a samar da yanayi mai kyau da zai bai wa kowa damar gudanar da kasuwanci cikin kwanciyar hankali da aminci.
Wannan kira na Sarkin Jinkan Hausawan Afrika na nuna cewa shugabanci na gaskiya yana nufin kare rayuka da amfanin jama’a, da kuma sanya ido wajen tabbatar da tsari da doka a kowanne mataki na al’umma.