News
Bincike: DSP Barau Shine Sanata Mafi Aiki Da Tasiri A Arewa
DAGA ABBA ANWAR
Wani bincike da ƙungiyar Indivisible Nigerian Project (INP), wadda ta ƙunshi ƙungiyoyi 27, ta gudanar, ya bayyana cewa Sanata Barau I. Jibrin shi ne sanata mafi tasiri daga Arewa a shekarar 2024 zuwa 2025.
Ƙungiyar ta fitar da wannan rahoto ne bayan wani taron shugabanni da ta gudanar a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, a cikin shirin bikin Ranar Dimokuraɗiyya da za a yi ranar 12 ga Yuni.
Sanata Barau Ya Kai Ziyara Kasuwar Waya Ta Farm Centre, Ya Ba Da Tallafi Naira Miliyan 200
A cikin wata wasika da Daraktan Arewa maso Yamma na ƙungiyar, Dr. Danjuma Monday Keffi, ya sanya wa hannu, an ce an gudanar da binciken ne domin tantance irin ayyukan da sanatocin Arewa suka gudanar, tare da duban yadda dokokin da suka gabatar ke shafar rayuwar jama’a.
SANATA BARAU BAI NUNA BANBANCI BA
Binciken ya nuna cewa Sanata Barau, wanda ke wakiltar Kano Arewa a Majalisar Dattawa, ya yi fice wajen gabatar da dokoki da ayyuka masu amfani ga jama’a ba tare da nuna banbancin kabila ko yanki ba.
WASU DAGA CIKIN DOKOKIN DA YA GABATAR SUN HAƊA DA:
Dokar Hana Laifukan Cyber Crime (2023)
Dokar kafa Kwalejin Fasaha ta Aghoro (Bayelsa, 2019)
Dokar kafa Kwalejin Ma’adinai ta Guyuk (2019)
Dokar kafa Jami’ar Nazarin Ruwa ta Ogharu (Anambra, 2019)
Dokar kafa Jami’ar Maritime ta Oron (2017)
BA MATSAYI KADAI BA, AKWAI AIKI
Duk da kasancewarsa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ƙungiyar ta ce abin da ya fi jan hankali shi ne irin ayyukan da Barau ke yi da kuma yadda dokokinsa ke samun amincewa cikin sauƙi daga gwamnati, musamman daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
WASU DAGA CIKIN DOKOKIN DA SUKA SAMU SAURIN AMINCEWA SUN HAƊA DA:
Sauya Kwalejin Fasaha ta Kabo zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha
Kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Rano
Sauya Kwalejin Ilimi ta Kano zuwa Yusuf Maitama Sule Federal University of Education
Kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC)
YANA SAURARON JAMA’ARSA
Wani rahoto daban da aka fitar kwanan nan ya ce Sanata Barau shi ne sanatan Arewa da yafi bayyana a kafafen yada labarai, yana kuma fiye da kowa wajen sanar da jama’arsa abin da ke gudana a Majalisa.
A cewar James Audu Dogo, Daraktan ƙungiyar, “Sanata Barau yana cikin ‘yan majalisa da suka fi tsayawa akan tuntuba da jama’a da kuma bayyana abubuwan da ke wakana.”
Rahoton ya nuna cewa ya samu maki 95 cikin 100 wajen yin tuntuba kai tsaye da mazabarsa, wanda ya sa ya sha bamban da sanatoci da dama.
Abba Anwar
Tsohon Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
✉️ fatimanbaba1@gmail.com
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
