Connect with us

News

Gobara Ta Ƙone Plaza A Kasuwar Farm Center A Kano

Published

on

Wata gobara mai ƙarfi ta tashi a fitacciyar kasuwar waya da ke Farm Center, Jihar Kano, inda ta ƙone wani sashi na ginin Plaza Dan Sulaika, tare da haddasa asarar kayayyaki masu daraja da aka kiyasta sun kai miliyoyin naira.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana a ranar Juma’a, lokacin da mafi yawan ‘yan kasuwar ke wajen gudanar da sallar Idi.

Kungiyoyin Fararen Hula 106 Sun Yi Kira Da A gudanar Da Bukukuwan Sallah cikin lumana A Kano

Wani shaidan gani da ido, Hassan Saminu, wanda shi ne ma’ajin ƙungiyar ‘yan kasuwar Farm Center, ya ce gobarar ta fara ne daga wani shago da ake amfani da batirin hasken rana, inda ake zargin matsalar haɗin wutar lantarki ta haddasa tashin gobarar.

“Da muka iso wurin, wutar ta riga ta bazu zuwa yawancin shaguna. Muna zargin wata matsala ce da ta faru tsakanin batirin solar da wutar lantarki,” in ji shi.

Ko da yake babu rahoton asarar rai, an ce an yi asarar kayayyaki da dukiyoyi masu tarin yawa, musamman wayoyi da na’urorin sadarwa.

Jami’an kashe gobara da na ceto sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka shafe sa’o’i suna kokarin shawo kan gobarar, lamarin da ya hana ta yaduwa zuwa wasu sassan kasuwar.

Advertisement

Plaza Dan Sulaika na daga cikin wuraren kasuwanci mafiya yawan hada-hadar kudi a cikin kasuwar  Farm Center, wadda ta shahara da sayar da wayoyi da kayan sadarwa.

Da aka tuntubi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce jami’an su da suka je wajen har yanzu ba su dawo ofis ba domin bayar da cikakken rahoto kan abin da ya faru.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending