Connect with us

News

Kungiyoyin Fararen Hula 106 Sun Yi Kira Da A gudanar Da Bukukuwan Sallah cikin lumana A Kano

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Kungiyoyi masu zaman kansu (CSOs) guda 106 da ke Kano sun bukaci al’ummar jihar, musamman matasa, da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali.

A cikin wata sanarwa da suka fitar, kungiyoyin sun taya Musulmi murnar zagayowar babbar Sallah (Eid-el-Kabir), tare da jinjina ga al’ummar Kano bisa yadda suka dade suna gudanar da bukukuwa cikin zaman lafiya da fahimtar juna.

Advertisement

DA DUMI-DUMI: Tsohon Babban Alkalin Ƙasa, Mohammed Uwais, Ya Rasu Yana Da Shekaru 89 A Duniya.

Sun ce: “A guji duk wani abu da zai iya tayar da hankali ko kawo tashin hankali, musamman daga matasa.”

Sun yi kira na musamman ga matasa da su kasance masu kishin kasa da al’umma, tare da nisantar barin kansu a yi amfani da su wajen tada zaune tsaye.

Advertisement

“Matasanmu su sani cewa su ne ginshikin gobe. Kada su bari wasu su cuce su ta hanyar basu naira su hana su makoma,” inji sanarwar.

Kungiyoyin sun nuna damuwa game da yadda wasu ke amfani da yanayin bukukuwan Sallah da sauran lokuta don janyo matasa cikin rikicin siyasa, tayar da hankali da yada kiyayya.

Advertisement

Sun bukaci ‘yan siyasa, masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma da su guji amfani da matasa a matsayin ‘yan daba ko kayan aikin tashin hankali. “Sallah lokaci ne na samun lada, ba na haddasa bala’i ba,” in ji sanarwar.

Haka kuma, sun bukaci hukumomin tsaro da su kasance cikin shiri don kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da yin aiki da kwarewa da gaskiya. “Zaman lafiya ba zai samu ba sai da hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, kungiyoyin fararen hula da al’umma.”

Advertisement

A karshe, sun bukaci malamai da shugabannin gargajiya da su rika jan hankalin jama’a wajen yada sako na zaman lafiya da juriya. Sun ce wannan lokaci ne da ya kamata kowa ya ji dadin bukin cikin salama da annashuwa.

> “Mu yi Sallah cikin lumana, mu guji tada hankali. Mu sanya juna a cikin adu’o’inmu. Kano na da kima, kada mu bari wani abu ya bata mata suna.”— Inji Hassan Ibrahim Gama da Mustapha Muhammed Chiroma, wadanda suka sa hannu kan sanarwar.

Advertisement

Sanarwar dai ta samu goyon bayan kungiyoyi 106 da suka hada da CDE, NEDIN, NAPWPD, MFI, VOHEDI, YEHDI, da sauran su.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending