News
Yadda Farfesa Sunusi Yakubu Ya Sauya Fuskar Kwalejin KCEPS A Kano
DAGA COMRADE BASHIR A. BASHIR
Farfesa Sunusi Ahmad Yakubu, wanda ke shirin kammala wa’adinsa a matsayin Provost na Kwalejin Koyar da Malanta da Karatun Farko ta Jihar Kano (KCEPS), ya bar tarihi mai armashi na sauye-sauye da ci gaba a harkar ilimi tun daga shekarar 2017.
An naɗa Farfesa Yakubu ne a lokacin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, kuma tun daga lokacin ya jagoranci kwalejin zuwa sabon matsayi da ya kara daraja da kima a idon al’umma da hukumomi.
Canjin Sunan Kwaleji da Inganta Takardun Shaida
Daya daga cikin manyan abubuwan da ya yi shi ne sauya sunan kwalejin daga College of Arts and Science (CAS) zuwa Kano State College of Education and Preliminary Studies (KCEPS). Wannan sauyi ya bai wa ɗalibai damar samun takardun NCE na hakika da gwamnati ke amincewa da su. Hakan ya sa suka fi samun damar ci gaba da karatu da kuma shiga kasuwar aiki cikin sauƙi.
Gine-gine Da Tallafin TETFund
A ƙarƙashinsa, kwalejin ta samu tallafi daga TETFund wanda ya taimaka wajen gina sababbin dakunan karatu, ajujuwa, da ofisoshi na zamani. Wannan ya kawo sauƙin gudanar da karatu da ayyukan ma’aikata.
Sabon Tsari Na Jagoranci
Ya ƙirƙiri sabon tsarin naɗa mataimakan Provost biyu – ɗaya kan harkokin NCE da ɗaya kan CEC – don tabbatar da daidaito da kulawa a aikin gudanarwa. Wannan shi ne karo na farko da aka samu irin wannan tsari tun kafa kwalejin a shekarar 1972.
Tallafa wa Malamai da Horo a Cikin Gida da Waje
KCEPS ta fara bayar da tallafin karatu ga malamai domin su samu ƙwarewa a matakan digiri da na digirin digirgir (PhD). Sama da malamai 50 ne suka amfana, inda masu digiri na biyu ke karɓar tallafi daga Naira miliyan 1.2 zuwa 1.5, yayin da masu PhD ke samun har Naira miliyan 4.5. Wasu kuma sun samu horo a ƙasashen waje kamar Amurka.
Kirkira da Fadada Dama ga Dalibai
Kwalejin ta fara amfani da tsarin e-learning wanda ke ba da damar yin karatu ta hanyar yanar gizo. Haka kuma, an buɗe annex campuses a wasu sassan Kano, musamman a Kunchi, inda aka kafa Ghari College of Education da ɗalibai sama da 100 ke karatun NCE. Kwalejin tana da ɗakunan kwana da ke sauke fiye da ɗalibai 360.
Sana’o’i Ga Matasan Da Ba Su Da Ilimin Boko
A kokarin rage zaman banza da tallafa wa matasa, kwalejin ta kafa shirin koyar da sana’o’i kamar dinki da sauransu ga matasan da ba su da ilimin boko. Wannan shiri na gudana ne a ƙarshen mako, kuma ana tattaunawa da Gwamnatin Kano domin yaɗa shi zuwa sauran kananan hukumomi.
Ƙarfafa Wakilcin Dalibai da Taimako Ga Marasa Galihu
Farfesa Yakubu ya kafa kungiyar ɗalibai ta kwaleji (Students Union Government – SUG) domin ba su damar fadin albarkacin bakinsu a harkokin kwaleji. Har ila yau, ya ba da tallafi ga ɗalibai marasa galihu da marayu domin su ci gaba da karatu cikin kwanciyar hankali.
ƙarshe Mai Daraja
Yayin da wa’adinsa ke zuwa ƙarshe, Farfesa Sunusi Yakubu ya bar gado mai muhimmanci ga kwalejin KCEPS – gado da ya haɗa da ci gaba a gine-gine, tsare-tsare, walwalar ma’aikata da samar da dama ga matasa a fannoni daban-daban na rayuwa.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
