Connect with us

News

Shugaban Amurka Trump Ya Yi Barazanar Kakaba Wa Kasashen Afirka Haraji

Published

on

Trump

Shugaba Donald Trump na Amurka ya shaida wa ‘yan jarida cewa yana shirin sanya harajin sama da kaso 10% kan kasashe masu tasowa, ciki har da na Afirka da yankin Caribbean.

Mista Trump ya ce zai yi wu a sa harajin bai daya ga kasashen, sannan ya kara da cewa harajin zai kasance ne kan kayayyakin da ke fitowa daga kasashe akalla 100.

Advertisement

Yadda Farfesa Sunusi Yakubu Ya Sauya Fuskar Kwalejin KCEPS A Kano

Shi ma Sakataren harkokin Kasuwancin Amurka Howard Lutnick ya ce kasashen da za a lafta wa wannan harajin suna cikin nahiyar Afirka da Caribbean.

Ko da yake ya kara da cewa kasashen ba su da muhimmanci sosai wajen cimma burin Trump na rage gibin kasuwanci da sauran kasashen duniya.

Advertisement

Tuni Trump ya aika da wasiku ga kusan kasashe fiye da ashirin da kuma Tarayyar Turai a wannan watan, inda ya shaida musu irin harajin da Amurka za ta fara cazarsu daga ranar daya ga watan Agustan 2025.

 

Advertisement

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending