Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 34 A  Jigawa.

Published

on

Akalla gidaje 34 ne suka rushe sakamakon ambaliyar ruwa da ta biyo bayan gagarumar ruwan sama da aka tafka a garin Jangari, da ke mazabar Rafin Marke a ƙaramar hukumar Garki, jihar Jigawa.

Ambaliyar, wadda ta auku cikin daren Lahadi, ta jefa ɗimbin mazauna garin cikin halin kunci, inda mutane da dama suka rasa matsugunansu tare da lalacewar kayayyaki da dama.

Advertisement

An binne marigayi Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura

Kansila mai wakiltar yankin, Malam Dayyanu Magaji Jangari, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin da shugaban ƙaramar hukumar Garki, Alhaji Adamu Hudu Kore, ya jagoranci wata tawaga ta jami’an gwamnati domin ziyarar jaje ga al’ummar da abin ya shafa.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce tuni an fara ɗaukar matakan rage raɗaɗin ibtila’in, tare da buƙatar gaggawar tallafi daga hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA), da sauran hukumomin da abin ya shafa.

Advertisement

Ya ce: “Mun zo nan da zuciya ɗaya domin nuna alhini da jajantawa al’ummarmu da ambaliya ta rutsa da su. Muna kuma neman tallafi da agaji daga dukkanin hukumomin da ke da alhakin taimakawa lokacin irin wannan bala’i.”

A cewar jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Garki, duk da cewar ba a samu asarar rai ba, har yanzu ba a tantance adadin kayayyakin da suka lalace ba sakamakon ambaliyar.

Advertisement

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da bibiyar lamarin domin tabbatar da cewa an ba waɗanda abin ya shafa kulawar da ta dace.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending