News
Hatsarin BMW Ya Yi Ajalin Babban Jami’in Ma’aikatar Kudi A Delhi
Wani babban jami’in Ma’aikatar Harkokin Tattalin Arziki ta Tarayyar Indiya, Navjot Singh, ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a yankin Delhi Cantonment a daren Lahadi. Hatsarin ya faru ne bayan wata mata mai tuƙi cikin sauri da mota kirar BMW ta buge babur ɗin da Singh ke tukawa tare da matarsa, Sandeep Kaur.
Rahoton ’yan sanda ya nuna cewa bugun ya jefa su kan hanya, inda Singh ya samu mummunan rauni da ya yi sanadin mutuwarsa a asibiti, yayin da matarsa ta tsira da karyewar ƙashi da kuma raunuka masu tsanani. Marigayin da matarsa sun taso ne daga wurin ibada na Bangla Sahib Gurdwara lokacin da lamarin ya faru.
Gwamna Bago Ya Sanya Dokoki Ga Malamai Masu Yin Wa’azi A Jihar Neja
Wani mutum da ya tsaya domin taimakawa, Mohammad Gulfam Hasan, ya ce shi ne ya ɗauke su zuwa asibitin New Life Hospital da ke Azadpur, mai nisan kilomita 19 daga inda hatsarin ya auku
Sai dai, matarsa ta marigayin ta bayyana a cikin ƙorafinta cewa duk da ta roƙi a kai su asibitin da ke kusa, sai aka ɗauke su zuwa wani asibiti mai nisa, inda ake zargin cewa akwai alaka tsakaninsa da iyalan wacce ke tuƙi da BMW ɗin. Wannan ya tayar da ƙarin ce-ce-ku-ce kan yadda aka gudanar da aikin ceto.
