News
Gwamna Bago Ya Sanya Dokoki Ga Malamai Masu Yin Wa’azi A Jihar Neja
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya bayyana cewa daga yanzu duk wani malami da ke son yin wa’azi a jihar wajibi ne ya mika hudubarsa a tantance kafin ya gabatar da ita.
Bago ya bayyana hakan ne a yayin wani shiri na gidan talabijin na TVC mai suna Politics on Sunday, inda ya ce matakin ba ya nufin hana wa’azi, sai dai don kaucewa hudubobin da ka iya kawo barazana ga tsaro da zaman lafiya.
Duk Gwamnonin Arewa Yayansu Suke Gina Wa, Ba Arewa Bace A Gabansu — Adnan Mukhtar
“Ba na hana wa’azi. Amma kowane mai huduba ya kawo nasa a tantance kafin ya yi amfani da shi. Wannan al’ada ce a wasu ƙasashe kamar Saudiyya. Ba za mu bari a yi wa’azi da zai saɓa wa jama’a ko gwamnati ba a ce komai daidai ne,” in ji shi.
Ya ce gwamnatin jihar na aiki kafada da kafada da jami’an tsaro ciki har da DSS, ’yan sanda, NSCDC da kuma sojoji domin tabbatar da an yi amfani da wannan doka yadda ya kamata.
Daraktan Harkokin Addinai na Jihar Neja, Umar Farooq, ya bayyana cewa duk malamin da ke sha’awar yin wa’azi dole ne ya nemi lasisi a cikin watanni biyu masu zuwa. Ya ce bayan cike fom, za a fuskanci kwamitin tantancewa kafin a ba da lasisin.
Sai dai wannan doka ta haifar da muhawara daga malaman addini daban-daban. Babban Limamin Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUT), Minna, Sheikh Bashir Yankuzo, ya ce yin wa’azi ibada ce, ba aikin gwamnati ba. Duk da haka, ya ce idan wani malami ya yi amfani da hudubarsa wajen tayar da fitina, gwamnati na da ikon tsoma baki.
Sakataren Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Neja, Raphael Opawoye, ya ce kungiyar ba ta samu wata sanarwa ta hukuma ba kan haramcin wa’azi, kuma za ta fitar da matsayinta ne idan aka sanar da ita a hukumance.
Shi kuwa wani malamin addinin Musulunci, Ustaz Uthman Siraja, ya bayyana matakin a matsayin kutse ga ’yancin yin ibada. Ya ce mafi dacewa shi ne gwamnati ta hukunta duk wani malami da ya yi hudubar da za ta iya jawo rikici maimakon kakabawa kowa wannan doka.
