Connect with us

News

Sai Ka Kalli Tallace-Tallace Kafin Ka Samu Takardar Bayan Gida A China

Published

on

684ffd2d7a3c9bdcb673d0e5

China ta ƙirƙiro wata sabuwar hanya mai ban mamaki domin takaita yawan asarar takardar bayan gida a wuraren jama’a – dole sai mai shiga bayan gida ya kalli tallace-tallace kafin ya samu takarda.

Wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna yadda ake amfani da na’urar zamani da aka girka a wasu bayan gidaje, wacce ba ta bayar da takarda sai an fara danna QR code ta waya, sannan a kalli gajeren tallan bidiyo. Bayan haka, na’urar za ta fitar da ƙaramin yanki na takarda. Ga wanda bai son kallon tallan ba, za a iya biyan kuɗi kusan kobo bakwai ($0.07) domin samun kowanne yanki.

Advertisement

Hatsarin BMW Ya Yi Ajalin Babban Jami’in Ma’aikatar Kudi A Delhi

Hukumomin kasar tun 2017 suka fara irin wannan tsarin, inda aka yi amfani da injin mai gane fuska da ke bayar da takarda sau ɗaya cikin minti tara. A 2019 kuma, aka ƙara amfani da fasahar AI da ke iyakance fitar da takarda sau ɗaya cikin minti goma ga kowanne mutum.

Sai dai wannan sabon tsarin na tallace-tallace ya haifar da muhawara da tambayoyi daga jama’a, musamman abin da zai faru idan mutum ya shiga bayan gida ba tare da waya ba, ko kuma batirin wayarsa ya ƙare.

Advertisement

A gefe guda, wasu na ganin wannan mataki hanya ce ta kare albarkatun ƙasa da hana asarar takarda. Amma a ɗaya ɓangaren, akwai masu ganin zai iya jefa mutane cikin damuwa, musamman a lokutan gaggawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending