Labarai
DA ƊUMI-ƊUMI: ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Yi Awon Gaba Da Dabbobi A Shanono

Wasu ’yan bindiga sun sake kai hari a garin Faruruwa, da ke yankin ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano, inda suka kashe mutum ɗaya tare da yin awon gaba da dabbobin al’umma.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan, waɗanda ake hasashen suna kan babura sama da guda 25, kowannensu ɗauke da mutum uku dauke da bindigogi
Shaidu sun ce maharan sun kai hari kan shagon waya, inda suka fasa shaguna suka kwashe wayoyi
Wani mazaunin yankin da ya shaida wa Premier Radio cewa al’ummar Faruruwa yanzu na cikin tsananin fargaba, suna kuma neman gaggawar taimakon jami’an tsaro domin kauce wa sake faruwar irin wannan mummunan lamari.
Hukumomin tsaro har yanzu ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba,
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
