News
Babu Mai Kishin Talakawa A Ƴan Siyasar Nijeriya Kamar Kwankwaso — Inji Waiya
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa babu ɗan siyasa a Najeriya da ke kishin talakawa kamar Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.
Waiya ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar domin taya tsohon Gwamnan Jihar Kano murnar cika shekaru 69 da haihuwa.
DA ƊUMI-ƊUMI: ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Yi Awon Gaba Da Dabbobi A Shanono
A cewar sanarwar, Kwamishinan ya taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa a madadin kansa, iyalinsa da dukkan ma’aikatan ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar.
Ya bayyana Dr. Kwankwaso a matsayin gwarzon ɗan siyasa mai hangen nesa, wanda ya ba da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban Kano da Najeriya baki ɗaya.
“Dukkanmu muna shaida irin namijin ƙoƙarin da Dr. Kwankwaso ya yi wajen inganta rayuwar al’umma — ta fuskar ci gaban ilimi, gina muhimman ababen more rayuwa, da kuma tallafawa dubban matasa wajen samun ilimi da sana’a,” in ji Waiya.
Kwamishinan ya kara da cewa kasancewarsa cikin gwamnatin da Kwankwaso ya kafa, abu ne da yake alfahari da shi, musamman ganin yadda jagorancin sa ya zamo abin koyi ga sauran jihohi.
A ƙarshe, Waiya ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Sanata Kwankwaso lafiya, hikima da hangen nesa, domin ci gaba da yi wa al’umma da ƙasar nan hidima cikin nasara.
