Connect with us

News

DA ƊUMI-ƊUMI: ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Yi Awon Gaba Da Dabbobi A Shanono

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Wasu ’yan bindiga sun sake kai hari a garin Faruruwa, da ke yankin ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano, inda suka kashe mutum ɗaya tare da yin awon gaba da dabbobin al’umma.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan, waɗanda ake hasashen suna kan babura sama da guda 25, kowannensu ɗauke da mutum uku dauke da bindigogi

Advertisement

Shaidu sun ce maharan sun kai hari kan shagon waya, inda suka fasa shaguna suka kwashe wayoyi

Wani mazaunin yankin da ya shaida wa Premier Radio  cewa al’ummar Faruruwa yanzu na cikin tsananin fargaba, suna kuma neman gaggawar taimakon jami’an tsaro domin kauce wa sake faruwar irin wannan mummunan lamari.

Advertisement

Hukumomin tsaro har yanzu ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba,

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending