News
Yan Bindiga Sun Sace Ma’aikaciyar INEC A Kogi
Wata ma’aikaciyar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta shiga hannun ‘yan bindiga a yayin da take tafiya a hanyar Aloma da ke cikin Jihar Kogi.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da ma’aikaciyar tare da wasu abokan aikinta ke kan hanyarsu daga Abuja zuwa Jihar Anambra domin shirye-shiryen zaben gwamna da ke tafe.
Jami’an ‘Yan Sandan Nijeriya Sun Kwato Motoci Biyu Da Aka Sato Daga Netherlands
Rahotanni sun ce maharan sun tare motar jami’an, suka bude musu wuta tare da tarwatsa gilashin motar. Duk da haka, babu wanda ya ji rauni sakamakon harbin.
An bayyana cewa ma’aikatan sun nufi Anambra ne domin buga rajistar masu kada kuri’a da wasu muhimman kayan da za a yi amfani da su a zaben gwamna da aka tsara zai gudana a farkon watan Nuwamba.
‘Yan bindigar dai sun yi awon gaba da dukkan fasinjojin da ke cikin motar, ciki har da direban da matarsa.
Kawo yanzu hukumomin tsaro ba su fito da cikakken bayani kan faruwar lamarin ba, yayin kokarin tuntubar mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Kogi ya ci tura.
