News
Na kashe Naira Biliyan 100 Bana Saboda Matsalar Tsaro — Gwamnan Borno
Gwamnan Jihar Borno dake Najeriya, Babagana Umara Zulum ya ce ya kashe kuɗaɗen da suka kai naira biliyan 100 a jihar sa, a wannan shekarar saboda tinkarar matsalolin tsaro kawai.
Zulum ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, Ali Ibn Mamza a fadar sa domin yi masa jaje dangane da wasu hare haren da aka kai wa mazauna yankin.
Nuna Bangaranci A Aikin Jarida Da Siyasar Kama Karya Na Kara Ta’azzara – Abdulbaqi Durumin Iya
Gwamnan ya kuma yaba wa jami’an tsaro saboda ceto wasu mutane 12 da aka yi garkuwa da su, waɗanda ɗaukacin su manoma ne mata.
Zulum ya ce ziyarar ta sa za ta ba shi damar samun cikakkun bayanai da kuma nazarin irin halin da ake ciki a yankin, domin ɗaukar matakan gyara a yankunan Askira da kuma Uba.
Gwamnan ya kuma bayyana ɓacin ran sa da yadda matsalar tsaron ke razana ƴan kwangilar da ake bai wa aiki a yankunan.
Daga bisani Zulum ya bayyana shirin samar da babbar makaranta da cibiyar zana jarabawar JAMB da asibiti da hanyoyi da kuma wasu kayayyakin more rayuwa a yankin.
Zulum wanda ya bayyana muhimmancin tsaro da kuma tasirin sa wajen zaman lafiya, ya bayyana matsalar da yake samu na gina hanyoyi a yankin daga ƴan kwangila, saboda haka ya ce zai samar da wurin fasa duwatsu da kuma sayen motoci 100 na ɗaukar kaya da za’ayi amfani da su wajen gina hanyoyin.
Sarkin Uba ya yaba wa gwamnan dangane da ziyarar da kuma ƙoƙarin da ya ke yiwa jama’ar yankin.
