Connect with us

News

Kano Online Chapel: Za Mu Ɗauki Mataki Kan Masu Ɓata Aikin Jarida  ‎ ‎— Dangambo

Published

on

Chairman KOMC Comrade Abubakar Dangambo 1200x1200
Shugaban Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo ta Kano Online Chapel da ke ƙarƙashin NUJ, Abubakar Abdulqadir Dangambo

 

 

Advertisement

Shugaban Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo ta Kano Online Chapel da ke ƙarƙashin NUJ, Abubakar Abdulqadir Dangambo, ya jaddada cewa za su ci gaba da jajircewa wajen kare ingancin aikin jarida tare da yin fatali da duk wani salo na gurbata Aikin.

Advertisement

‎Dangambo ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a jihar Kano, a ranar Juma’a, inda ya nuna damuwarsa kan yadda wasu ‘yan jarida ke amfani da sunan Kano wajen wallafa rahotannin da ke ɗauke da  batanci ga  mutane da kuma  cibiyoyi.

Advertisement

‎Ya ce, “Aikin jarida yana buƙatar daidaito. Ba za ka ɗauki gefe ɗaya ka bar ɗaya ba, musamman a labaran da ke ƙunshe da sarkakiya. Rashin yin hakan na sanya  zargi ga Aikin Yan Jarida.

Advertisement

‎Shugaban ya bayyana cewa akwai wasu editoci a wasu gidajen jarida na yanar Gizo da ke amfani da sunayen bogi wajen yi wa mutane kazafi, wanda ya ce hakan ya saba wa ƙa’idojin aikin jarida.

Advertisement

‎“Abin takaici ne cewa wasu suna fakewa da sunan Kano wajen wallafa labaran da ba su da tushe balantana makama. Wannan ya sabawa ladubban aikin jarida kuma ba za mu amince da hakan ba,” in ji shi.

Advertisement

‎Dangambo ya ce Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo  ba dalili ba ne na kauce wa bin ƙa’idojin NUJ ba.

Advertisement

‎Ba za mu ci gaba da kallon yadda wasu ke aikata abin kunya a fannin jarida ba, domin jama’a na iya ɗauka cewa dukkanmu iri ɗaya ne,” in ji shi.

Advertisement

‎Ya ce kungiyar na aiki wajen fitar da jerin sunayen sahihan mambobinta don bambance su da waɗanda ke aikata abin da ya saba wa ka’ida.

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending