News
Gwamnatin Kano Ta Ce Yin Goyo Da Sunan Achaba Kawai Aka Hana A Fadin jihar
Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude (SAN), ya gana da Kwamishinan ’Yansanda na Jihar Kano a ranar Juma’a domin tattauna wa kan koke-koken jama’a kan kamun masu babura da ake yi a fadin jihar.
Taron ya mayar da hankali ne kan duba yadda ake aiwatar da Dokar hana Achaba ta 2013, tare da jaddada cewa dole a tabbatar da cewa duk wani aikin tsaro yana gudana cikin bin doka ba tare da tauye hakkin direbobin babura da ba na Achaba ba.
Kano Online Chapel: Za Mu Ɗauki Mataki Kan Masu Ɓata Aikin Jarida — Dangambo
Mai taimaka wa kwamishinan shari’a kan harkokin yada labarai, Abubakar Tijjani Ibrahim, ya ce tattaunawar ta yi nufin karfafa hadin kai tsakanin Ma’aikatar Shari’a da Rundunar ’Yansanda domin tabbatar da sahihin aiwatar da doka cikin gaskiya da adalci.
Ya kara da cewa za a fitar da cikakkun bayanai kan sakamakon ganawar a nan gaba.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
