Connect with us

News

Noman Rani Na Fuskantar Barazana A Najeriya Sakamakon Tsadar Taki

Published

on

Spread the love

Noman rani a Najeriya na fuskantar babbar barazana sakamakon tsadar kayan noma, musamman taki da sauran muhimman abubuwan da manoma ke amfani da su, a wani lokaci da farashin amfanin gona a kasuwanni ya faɗi warwas.

Manoma a sassa daban-daban na ƙasar sun bayyana damuwa cewa hauhawar farashin taki, iri, magungunan kashe ƙwari da man fetur na iya kawo cikas ga noman rani, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci da rage ƙarancin kayan masarufi a lokacin rani.

A cewar wasu manoma da Fri Hausa ta zanta da su, farashin buhun taki ya kai wani matsayi mai tsanani, inda wasu ke cewa yana ninkawa sau biyu zuwa uku fiye da yadda aka saba, lamarin da ya sa da yawa ba za su iya noma yadda suka tsara ba.

“A wannan lokaci da muke fatan noman rani zai taimaka mana mu gyara asarar da muka yi, sai ga shi farashin kayan noma ya tashi sama, yayin da farashin hatsi da kayan lambu a kasuwa ke ta faɗuwa,” in ji wani manomi a jihar Bauchi.

Advertisement

Manoman sun ce wannan yanayi na iya janyo ƙarancin amfanin gona a watanni masu zuwa, tare da yiwuwar ƙara tsadar abinci a faɗin ƙasar, idan har gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba.

Masana harkar noma na gargadin cewa ci gaba da watsi da matsalar tsadar kayan noma na iya kassara noman rani, wanda ke da muhimmanci wajen cike gibin abinci da samar da ayyukan yi ga dubban matasa a yankunan karkara.

A halin da ake ciki, manoman na kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da su tallafa musu ta hanyar rage farashin taki, inganta rarraba kayan noma, da kuma samar da sauƙaƙan rance, domin ceto noman rani daga durƙushewa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *