News
Kana Gani Kasan Asiri Za A Yi Da Makogwaron Ladanin Masallacin Da Aka Cire A Kano — Jami’an ‘Yan Sanda
An yi zargin wani mutum da yanka makogaran wani Ladani mai suna Malam Zubairu a Masallacin Yusuf Garko da ke yankin Maraba a unguwar Hotoro da ke birnin Kano wanda ya yi sanadiyar rasa ransa.
Ganau sun ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Litinin, inda wanda ake zargin ya yanka makogaran Ladanin lamarin da ya fusata al’ummar yankin.
Jami’an Tsaro Sun Yi Nasarar Kuɓutar Da Mutum 3 Da Aka Sace A Kano
An zargin wasu mazauna yankin dai, sun bi wanda ya aikata lamarin tare da kashe shi.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da an kashe matashin da ya aikata kisan gilla ga ladanin da kuma cire masa makogwaro.
Inda ta bayayana cewa an dawo da zaman lafiya a yankin bayan tura jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda.
A cewar ’yansanda, tawagar bincike ta gano makogwaron mamacin a cikin aljihun wanda ake zargin.
Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin tabbatar da an hukunta duk wanda ke da hannu a ciki.
-
News18 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
