Connect with us

News

Jami’an Tsaro Sun Yi Nasarar Kuɓutar Da Mutum 3 Da Aka Sace A  Kano

Published

on

An yi wata musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da tawagar dan ta'adda Bello Turji
Spread the love

Jami’an tsaro na hadin-gwiwa karkashin ‘Operation MESA’ sun ceto mutum uku daga cikin mutane biyar da aka sace a lokacin wani harin ‘yan bindiga da daddare a karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.

Rundunar ta hadin-gwiwa ta hada da sojojin rundunar soji ta 3, rundunar sojin sama ta Nijeriya (NAF) da rundunar ‘yansandan Nijeriya (NPF).

Arewa Rents na Sauya Harkar Cinikayyar Kadarori a Arewacin Najeriya ta Hanyar Fasahar Zamani

LEADERSHIP ta ruwaito cewa, an sace mutanen ne a daren Lahadi lokacin da wasu mutane dauke da makamai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai hari a kauyen Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo.

Da yake martani kan lamarin, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar soji ta 3, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya tabbatar da ceto mutane uku, daga cikin wadanda aka sace yayin da ake ci gaba da kokarin ceto sauran biyun.

Advertisement

Kyaftin Zubairu ya tabbatar wa jama’a cewa, rundunar ta hadin gwiwa sun kuduri aniyar ceto dukkan mutanen da aka sace cikin koshin lafiya.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *