Connect with us

News

Jami’an Yan Sanda Sun Sanar Da Dawo Da Aiwatar Da Dokar Lasisin Gilashin Mota Mai Duhu

Published

on

tinted glasses.png 1
Spread the love

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta sanar da cewa za ta sake fara aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu (Tinted Glass Permit), tana mai cewa babu wani umarnin kotu da ke hana ta ɗaukar matakin a halin yanzu.

Rundunar ta ce matakin ya zama wajibi ne sakamakon ƙaruwa da ake samu na laifuffukan da ake aikatawa ta amfani da motocin da ke da gilashi masu duhu ba tare da izini ba.

Noman Rani Na Fuskantar Barazana A Najeriya Sakamakon Tsadar Taki

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa dakatarwar da aka yi a baya ta kasance ne domin bai wa masu ababen hawa damar daidaita takardunsu, ba wai saboda umarnin kotu ba.

“Babu wata umarnin kotu da ke hana rundunar aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu,” in ji Hundeyin.

Advertisement

A cewarsa, bayanan tsaro sun nuna cewa wasu mutane da ƙungiyoyin aikata laifi na amfani da motocin bakin gilashi marasa izini wajen ɓoye fuskokinsu, lamarin da ke sauƙaƙa aikata laifuka kamar fashi da makami, sace-sace da kuma garkuwa da mutane.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rundunar ta dakatar da aiwatar da dokar ne a baya biyo bayan wata shari’a da aka shigar a kotu, domin bai wa masu motoci damar kammala takardunsu.

Sai dai rundunar ta jaddada cewa sake fara aiwatar da dokar ya biyo bayan nazari kan halin tsaro da kuma buƙatar kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Rundunar ta ƙara da cewa Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya ba da tabbacin cewa za a gudanar da aikin cikin kwarewa, tare da mutunta haƙƙin ’yan ƙasa da bin doka yadda ya kamata.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *