News
Sai Da Buhari Ya Gasgata Cewa Ina Son Kashe Shi —Aisha Buhari
Uwargidan tsohon shugaban ƙasa, Aisha Buhari ta bayyana cewa marigayi mijinta, Muhammadu Buhari, ya taɓa fara kulle ƙofar ɗakinsa sakamakon jita-jitar da ta karade fadar Aso Rock cewa ita ce ke shirin kashe shi.
Wannan bayani na A’isha Buhari ya fito ne a cikin sabon littafin tarihin rayuwar Buhari mai shafi sama da 600, mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Dr. Charles Omole ya rubuta, kuma aka ƙaddamar da shi a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Litinin.
Jami’an Yan Sanda Sun Sanar Da Dawo Da Aiwatar Da Dokar Lasisin Gilashin Mota Mai Duhu
Aisha ta ce matsalar rashin lafiyar da ta sa Buhari ya shafe kwanaki 154 yana jinya a ƙasashen waje a shekarar 2017 ta samo asali ne daga lalacewar tsarin cin abinci da kuma rashin kula da abinci yadda ya kamata.
A cewarta, rashin lafiyar Buhari ba wata cuta ce mai ban tsoro ko guba ba, kamar yadda wasu ke yadawa a wancan lokaci.
