News
Tsohon Babban Alkalin Alkalan Najeriya Tanko Muhammad Ya Rasu
Tsohon Babban Alƙalin Ƙasa (CJN), Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad (mai ritaya), ya rasu a wani asibiti da ke Ƙasar Saudiyya.
Wata majiya ta tabbatar da cewa marigayin ya rasu da safiyar Talata, lamarin da ƙungiyar dalibai musulmai na fannin shari’a ta NAMLAS ta tabbatar a wata sanarwar ta’aziyya da ta fitar a Abuja ranar 16 ga Disamba, 2025.
Sai Da Buhari Ya Gasgata Cewa Ina Son Kashe Shi —Aisha Buhari
NAMLAS ta bayyana rasuwarsa a matsayin babbar rashi ga bangaren shari’ar Nijeriya da sana’ar lauya da al’ummar Musulmi da ƙasa baki ɗaya, tana mai bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya da tawali’u da jajircewa wajen tabbatar da adalci.
Ƙungiyar ta ce marigayin ya gudanar da aikinsa da hikima da biyayya ga doka, tare da barin kyakkyawan tarihi da zai ci gaba da zama jagora ga al’ummomin lauyoyi na gaba.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
