News
Dangote Ya Shigar Da Shugaban NMDPRA Kara Gaban ICPC Kan Zargin Biyawa Yayansa Dala Miliyan 5 Kudin Makaranta
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya shigar da ƙorafi ga hukumar ICPC kan shugaban hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa NMDPRA, Ahmed Farouk, bisa zargin cin hanci da rashawa.
Ƙorafin, wanda ke ɗauke da kwanan wata 16 ga Disamba, 2025, an miƙa shi ta hannun lauyan Dangote, Ogwu Onoja, SAN, kuma ofishin Shugaban ICPC, Musa Aliyu, SAN, ya karɓa.
APCn Kano Cikin Sarkakiyar Dimauta : Yayin Da Kulle-Kulle Kan DSP Barau Ke Kara Ta’azzara
Dangote ya zargi Ahmed Farouk da rayuwa fiye da albashinsa a aikin gwamnati, inda ya ce shugaban ya kashe sama da dalar Amurka miliyan biyar wajen biyan kuɗin karatun ƴaƴansa huɗu a makarantun sakandare a ƙasar Switzerland.
A cewar ƙorafin, an biya kuɗaɗen karatun ne gaba ɗaya na tsawon shekaru, abin da Dangote ya ce ba zai yiwu a tabbatar da shi daga halal ɗin kuɗin shiga da Farouk ya samu a duk tsawon aikinsa na gwamnati ba.
Attajirin ya zargi Farouk da saɓawa ƙa’idojin aikin gwamnati, tare da zargin shi da tara dukiya ta haramtacciyar hanya, cin zarafin ofis, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
Dangote ya ƙara da cewa shugaban NMDPRA ya yi amfani da ikonsa wajen wawure wa da karkatar da kuɗaɗen jama’a domin amfanin kansa da na wasu yan tsiraru, lamarin da ya ce ya haifar da fushin jama’a da zanga-zanga.
Ya bayyana sunayen ‘ya’yan huɗun da abin ya shafa, makarantu a Switzerland da suke karatu, da kuma adadin kuɗin da aka ce an biya, tare da roƙon ICPC ta bincika gaskiyar zarge-zargen.
