News
Gidauniyar Kashe Kwabo ta Gudanar da Aikin Idanu da Kaciya ga Ya’yan Marayu 602 Kyauta A Kano
DAGA YAZID SUNUSI YAHAYA
Wata Gidauniyar Jin kai mai suna (Kashe Kwabo Foundation), ta samar da kwararrun Likitoci domin aikin idanu ga masu rauni da yi wa ‘ya’yen marayu kaciya kyauta a jihar Kano.
Da muke zantawa da shi a Asibitin Sarkin Dori Sulaimanu da ke Unguwar Lokon Maƙera, Kofar Na’isa, in da ake gudanar da aikin, Shugaban Gidauniyar Alhaji Yusuf Umar Kashe Kwabo ya ce suna gudanar da aikin a wasu muhimman sassa na jihar Kano. Shugaban ya ce baya ga aikin idon su kan bawa manya mutane gilashin ƙara gani musamman ga masu yin karatun zamani ko na addini.
Jami’an NDLEA Sun Kama Indiyawa 22 Bisa Zargin Shigo Da Hodar Ibilis Najeriya
Kashe Kwabo, ya ce ya zuwa haɗa wannan rahoton Gidauniyar ta ƙaddamar da aikin ido da bayar da gilashin karatu da magani ga masu larurar ciwan idanu ga mutane 300.
Haka kuma sun samu nasarar yi wa ‘ya’yen marayu kaciya su 200 a wannan lokaci na sanyi da nufin sauƙaƙa wa iyayensu duba da yanayi na rayuwa da kuma neman ƙara kusaci ga Allah Madaukakin Sarki.
Ya ce waɗanda aka tarar yanar ido ke garesu ana ɗaukan su zuwa asibitin da aka ware domin yi musu aiki lokaci-bayan-lokaci duk yawansu har a kammala, kuma kyauta in ji shi.
Ya yi ƙarin haske game da aikin ” Yadda muka tsara aikin shine Kaciya da kuma Aikin idanu za a yiwa mutum 820 ne kuma har izuwa sanda muke tattara al’ƙalima mu ansamu jumillan Kaciya 202 da Kuma aikin ido 400″.
Yusuf Kashe Kwabo ya barranta aikin da siyasa ” Duk da jama’a na kallona a matsayin ɗan siyasa kuma shugaban jamiyyar APC na ƙaramar hukumar Gwale, wannan aikin ba na siyasa ba ne, kuma babu siyasa a cikin ayyukan da muke yi, muna zama mu kiyaye ƙudurinmu na taimakawa marayu da marasa ƙarfi daga cikin al’ummr mu”. Ina ji shi.
Ya ƙara jaddada cewa aikin nasu duk jihar Kano ya ƙunsa wanda suka rarrabashi ga duk ƙungiyoyin da suke tare da su a kowane sashi na jihar.
Alh. Sani Yahaya Lokon Maƙera na daga cikin waɗanda suka amfana da shirin, ya ce bayan an duba idanunsa an kuma bashi gilashin ƙara gani, don haka ya nuna farin cikin samun wannan Gidauniya, Kuma yace zai cigaba da karatu da gilashin da aka bashi Inshallah tare da gode wa wanda ya samar da wannan abin alhairi.
Hadiza Uba Abdullahi Kabara tayi godiya bisa samun Gilashin ƙarin gani wanda ta ce zai taimaka mata wajen gudanar da ayyukan ta batare da damuwa ba, ta gode wa Allah gami da addu’a ga wandanda ke da hannu wajen samar da wannan shiri mai albarka.
Hajiya Hadiza ta roƙi mawadata daga cikin al’umma da su yi koyi da Gidauniyar, a rinƙa taimakawa masu rauni musamman ta fanin lafiya saboda muhimmancinta ga ɗan adam ga kuma rayuwa ta yi tsada.
