Connect with us

News

‎Halin Da Venezuela Ta Faɗa Izina Ne Ga Masu Kiran Amurka Ta Kaiwa Najeriya Ɗauki ‎ ‎ ‎—MURIC ‎

Published

on

tinubu and trump 750x536 (1)
Spread the love

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi, a Najeriya Muslim Rights Concern (MURIC), ta gargaɗi ƴan ƙasar da su guji kiran Amurka ta tsoma baki a harkokin cikin gida, tana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rikicin makamancin wanda Venezuela ke fuskanta.

‎Daraktan zartarwa na ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, yana mai kira ga ƴan Nijeriya da su koyi muhimman darussa daga abubuwan da ke faruwa a Venezuela.

Jami’an NDLEA Sun Kama Indiyawa 22 Bisa Zargin Shigo Da Hodar Ibilis Najeriya 

‎Akintola ya danganta lamarin da rahotannin wani aikin soja da Amurka ta kai a Venezuela, inda aka kama Shugaban ƙasar, Nicolás Maduro, tare da iƙirarin cewa an ɗauki matakai na karɓe iko da arzikin man ƙasar.

‎A cewarsa, an yi amfani da hujjar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ne a matsayin rufe gaskiyar muradin tattalin arziki, musamman man fetur.

Advertisement

‎MURIC ta kuma yi watsi da abin da ta kira labarin “kisan Kiristoci” a Nijeriya, tana gargaɗin cewa irin wannan zance na iya zama uzuri na tsoma bakin ƙasashen waje.

‎Ƙungiyar ta ambaci hare-haren tsaro da suka shafi al’ummomin Musulmi a wasu jihohi, tana cewa hakan na ƙaryata iƙirarin wariya ta addini.

‎Farfesa Ishaq ya kuma bukaci ƴan ƙasar da suka zama masu haɗin kai da kuma kare albarkatun ƙasar.

‎A cewarsa, Nijeriya ta tsallake hatsari ne kawai saboda hankalin Amurka ya karkata zuwa Venezuela, wadda ke da manyan rijiyoyin mai fiye da Nijeriya, sai dai ya gargaɗi cewa hakan ba yana nufin Najeriya ta fita daga haɗari gaba ɗaya ba, muddin ake ci gaba da yaɗa labaran da ke neman tsoma bakin ƙasashen waje.

Advertisement

‎A ƙarshe, MURIC ta yi kira ga shugabanni, malamai da sauran masu faɗa a ji da su yi taka-tsantsan wajen kalamansu, tare da fifita zaman lafiya, fahimtar juna da kare ikon ƙasa.

‎Ƙungiyar ta ce ya zama wajibi ƴan Nijeriya su kalli matsalolinsu a matsayin na cikin gida da za a warware ta hanyar haɗin kai da adalci, ba ta hanyar neman agajin ƙasashen waje ba, domin hakan na iya jefa ƙasar cikin babbar barazana ga tsaro, tattalin arziki da ƴancin kai.

 

RFI

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *