News
Gwamnatin Bauchi Ta Rufe Kasuwannin Shanu 25 A Faɗin Jihar
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayar da umarnin dakatar da dukkan harkokin kasuwanci a kasuwannin shanu 25 da ke ƙananan hukumomin Bauchi, Tafawa Balewa, da Kirfi da Alkaleri, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro da ake dangantawa da aikata laifuka.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar, an ce matakin ya biyo bayan rahotannin tsaro da suka nuna cewa wasu daga cikin kasuwannin sun zama mafaka ga masu aikata laifuka.
JAMB Ta Sanya Ranar Da Za A Fara Jarabawar UTME Ta 2026
Sanarwar ta lissafa kasuwannin da abin ya shafa a Alkaleri da suka haɗa da Alkaleri, da Mansur, da Futuk, da Yalo, da Gwana, da Yalon Gurza, da Kuka, da Rimi, da Pali, da Bokwas, da Kwaimawa, da Mai-Ari, da Gajin Duguri da Maina Ma’aji. Haka kuma an rufe kasuwar Liman Katagum a Bauchi, yayin da a Kirfi aka dakatar da Lariski, da Bara, da Sharfuri, da Cheledi da Boli, sai kuma Burga, da Bununu, da Ball, da Kulumbo da Zwall a Tafawa Balewa.
Gwamnan ya bayyana cewa bayanan sirri sun nuna kasuwannin sun zama cibiyoyin aikata laifuka irin su satar shanu, da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, da kisa da kuma karɓar kuɗaɗen haram. Ya kuma nuna damuwa kan zargin cewa ana amfani da wuraren wajen safarar makamai da hada-hadar kuɗaɗen haram.
Ya ce matakin na wucin gadi ne kuma zai ci gaba har sai an samu gagarumin sauyi a harkokin tsaro. Ya umarci jami’an tsaro su tabbatar da cikakken bin dokar, yayin da ya ɗorawa ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya alhakin wayar da kan jama’a da sa ido, tare da kira ga al’umma su ba da haɗin kai domin dawo da zaman lafiya da kare harkokin tattalin arziƙi a jihar.
