Politics
Dan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar PDP Amb. Muhammad Bello Dalha ya Matar Da Form Din Takararsa
Dan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar PDP Amb. Muhammad Bello Dalha ya Matar Da Form Din Takararsa
Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP, Dakta Ambasada Muhammad Bello Dalha, ya mayar da fom din neman tsayawa takarar gwamnan jihar domin fafatawa a zaben 2027 mai zuwa.
Amb. Muhammad Bello Dalha Ya Sayi Fom Din Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar PDP
Ambasada Muhammad Bello Dalha ya mayar da fom din ne da yammacin ranar Talata a sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa da ke Abuja, inda ya bayyana kudirinsa na kawo sauyi da ci gaba a jihar Kano.
Da yake jawabi bayan mika fom din, Dalha ya ce ya dauki matakin tsayawa takarar ne bayan dogon nazari da ya yi kan kalubalen da jihar Kano ke fuskanta, musamman matsalolin rashin tsaro, durkushewar masana’antu da kuma matsin rayuwa da al’umma ke ciki.
Ya bayyana cewa takararsa wata sabuwar tafiya ce ta jam’iyyar PDP domin dawo da martabar jihar Kano ta hanyar samar da ci gaba mai dorewa a fannoni daban-daban.
Dan takarar ya yi alkawarin mayar da hankali wajen inganta harkar ilimi, samar da tsaftataccen ruwan sha, bunkasa tsaro da kuma raya yankunan karkara domin inganta rayuwar al’umma.
Hakazalika, ya jaddada aniyarsa ta tabbatar da adalci da yaki da duk wasu ayyukan bata-gari da ka iya tarnaki ga zaman lafiya da cigaban jihar.
Ambasada Muhammad Bello Dalha ya kuma yi alkawarin samar da guraben ayyukan yi ga matasa, bunkasa sana’o’in hannu tare da bai wa mata da matasa masu tasowa tallafin jari domin dogaro da kai.
A cewarsa, idan aka ba shi dama, gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru wajen ganin Kano ta sake zama abar koyi a Arewa da ma Najeriya baki daya..
