Connect with us

News

Gwamnatin Legas Ta Kwace Baburan Okada  Sama Da 300

Published

on

FVdsP7LWIAAFLfS

Gwamnatin legas ta kwace baburan okada guda 309 yayin wani samamen hadin gwiwa da ta gudanar a kan hanyar Legas- zuwa Badagry Expressway domin tabbatar da tsaro, rage cunkoson ababen hawa da kuma aiwatar da dokokin jihar.

Samamen ya gudana ne tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ruwa ta Jihar Legas da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, inda jami’an suka kuma rusa rumfuna da gine-ginen da aka kafa ba bisa ka’ida ba tare da dakile kasuwanci a kan tituna da sauran ayyukan da suka saba wa dokokin muhalli.

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Mutum Bisa Zargin Dukan Matarsa Har Ta Lahira Saboda Ta Ƙi Dafa Abinci 

Mai magana da yawun Hukumar Task Force, Abdulraheem Gbadeyan, ya ce aikin wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da hana masu aikata laifuffuka fakewa da harkokin kasuwanci wajen gudanar da miyagun ayyukansu.

Ya bayyana cewa samamen ya gudana a wurare da dama da suka hada da Orile-Iganmu, Suuru-Alaba, Mile 2 Underbridge, Mazamaza, Festac First Gate, Iyana-Ira, Abule-Ado, Alakija, Iyana-Iba, Alaba Rago, Old Ojo Road da Okoko Bus Stop.

A cewarsa, an kwace baburan haya guda 309, sannan jami’an sun cire kayayyakin da suka tare hanyoyi, rusa bukkoki da rumfunan da aka gina ba bisa ka’ida ba, tare da kawar da sauran abubuwan da ke hana zirga-zirgar jama’a.

Advertisement

Gbadeyan ya ce matakin ya taimaka wajen bude hanyoyi, inganta zirga-zirgar ababen hawa da kuma tabbatar da tsaftar muhalli a yankunan da abin ya shafa.

Ya kara da cewa za a bi tanadin Dokar Gyaran Sashen Sufuri ta Jihar Legas ta 2018 wajen neman kotu ta amince da kwace baburan da aka kama saboda karya dokar da ta haramta zirga-zirgar baburan haya a wasu manyan hanyoyin jihar .

 

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending