Connect with us

News

MURNAR CIKA SHEKARU 58: Juriya Da Haƙurin Yilwatda Sun Ƙara Wa APC Ƙarfi A Najeriya – Kwankwaso

Published

on

IMG 20260809 150118 813

DAGA MUHAMMAD KABIR, KANO

Daraktan Kudi na Hukumar Hadejia Jama’are River Basin Development Authority, Dr. Musa Illiyasu Kwankwaso, ya ce jajircewa, haƙuri da kuma salon jagorancin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshen Yilwatda, sun taimaka wajen ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a saƙon taya murnar cika shekaru 58 da haihuwa da ya aike wa Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshen Yilwatda.

Kano: Gini Ya Rufta Kan Mutane 16 Ciki Har Da Yara Shida

Ya ce Yilwatda ya nuna ƙwarewa da jajircewa wajen jagorantar jam’iyyar, musamman ta hanyar ƙarfafa haɗin kai, bai wa kowa dama da kuma tabbatar da dimokuraɗiyya a cikin APC.

A cewar Kwankwaso, ƙoƙarin shugaban jam’iyyar wajen ƙarfafa tsarin APC da faɗaɗa yawan mambobinta ya taimaka wajen ƙara mata ƙarfi a faɗin ƙasar.

Advertisement

Ya kuma yaba wa Yilwatda bisa irin goyon bayan da yake bai wa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman shirin Renewed Hope Agenda, da kuma ƙoƙarin inganta shugabanci da ci gaban ƙasa.

“Shugaban APC na Ƙasa ya kasance jagora mai kishin ci gaban jam’iyya. Gudunmawarsa wajen ƙarfafa jam’iyyar ta taimaka wajen tabbatar da haɗin kai, bai wa kowa dama da kuma inganta dimokuraɗiyya a cikin APC,” in ji shi.

Kwankwaso ya ƙara da cewa ƙoƙarin Yilwatda na haɗa kan ‘yan jam’iyya da kuma faɗaɗa tsarin APC ya fara haifar da sakamako mai kyau, yana mai cewa jam’iyyar na da kyakkyawan matsayi gabanin zaɓukan da ke tafe.

Ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Farfesa Yilwatda lafiya, hikima da ƙarfin guiwa, tare da ba shi tsawon rai domin ci gaba da hidimtawa jam’iyya da ƙasa.

Da yake magana kan siyasar Arewa, Kwankwaso ya ce ’yan yankin sun amince da manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu, yana mai cewa APC na iya samun gagarumin goyon baya a zaɓukan da ke tafe.

Ya ce: “A Arewa, Shugaban APC na Ƙasa ya kamata ya kwanta barci cikin kwanciyar hankali, domin ’yan Arewa sun amince da kyakkyawan shugabancin Shugaba Tinubu, kuma sun shirya bai wa shi da sauran ’yan takarar jam’iyyar gagarumin goyon baya.”

Advertisement

A Kano, Kwankwaso ya ce yana da yakinin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ’yan takarar APC na Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jihar Kano za su samu nasara a zaɓukan da ke tafe.

Ya kuma gode wa Shugaban APC na Ƙasa bisa hikimarsa da ƙoƙarinsa na tabbatar da haɗin kan jam’iyyar tare da mayar da ita babbar jam’iyya mai ƙarfi a ƙasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending