Connect with us

News

Rikicin Hausawa da kabilar Berti ya ci sama da mutum 100 a Sudan

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumomin jihar Blue Nile da ke kudu maso gabashin Sudan sun ce mutum 105 ne aka tabbatar sun rasa ransu a rikici kan filaye da aka shafe kwanaki ana yi.

 

Advertisement

Ministan lafiya na jihar ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa, yanzu hankali ya kwanta amma yadda za a yi da mutanen da rikicin ya raba da gidajensu ita ce matsalar.

Ƴan vigilante sun cafke matasa da su kankware wajen satar awaki a

Advertisement

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum dubu 15 ne suka tsere daga muhallansu a jihar ta Blue Nile, kuma da yawa daga cikinsu sun samu mafaka ne a makarantu.

 

Advertisement

Rahotonni sun ce rikici tsakanin Hausawa mazauna ƙasar da kuma ‘yan ƙabilar Berti ya faro ne ranar Litinin kan rikicin mallakar filaye.

 

Advertisement

Sai dai kuma wasu na cewa fadan ya tashi ne a sanadiyyar nadin sarautar gargajiya da aka yi wa Hausawa.

 

Advertisement

Majalisar ta ce a fadin kasar ta Sudan sama da mutum miliyan 14 ne ke bukatar taimakon gaggawa, amma kuma tana matukar karancin kayan taimakon.

 

Advertisement

Rikicin na Blue Nile ya haddasa zanga-zanga a tituna a biranen kasar ta Sudan, inda har aka sanya dokar hana fita a biyu daga cikinsu a farkon makon nan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending