Connect with us

News

Da Yiwuwar DSS Da Take Tsare Da Mamu Ta Gurfanar Da Shi A Gaban Kotu Ranar Litinin

Published

on

DAGA  KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Alamu sun bayyana a karshen makon da ya gabata cewa mai yiwuwa a gurfanar da wanda yake shiga tsakanin da ‘yan bindiga Wajen ganin an sakon fasinjojin jirgin kasan kaduna zuwa Abuja da ake tsare da shi, Tukur Mamu a gaban kotu a Abuja ranar Litinin mai zuwa.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS wanda ke hannun ta, ta kuma hana lauyoyi da ‘yan uwa ganin mawallafin jaridar Desert Herald, wanda jami’an hukumar suka kama a makon jiya.

Advertisement

’Yan Najeriya Miliyan 60 Na Fama Da Tabin Hankali

A ranar Talatar da ta gabata ne aka kama Mamu, matansa biyu da ‘ya’yansa maza biyu a kasar Masar a lokacin da suke zuwa aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Advertisement

Bayan tsare su na tsawon awanni 24 a birnin Alkahira, jami’an tsaro na farin kaya DSS sun kore su tare da kama su a lokacin da suka isa filin jirgin sama na Aminu Kano da ke jihar Kano.

Wata majiya ta iyali ta ce tawagar lauyoyin karkashin jagorancin Barista Sani Ningi dai yana hedikwatar DSS da ke Abuja domin ziyartar Tukur Mamu amma an hana shi ganawa da shi.

Advertisement

Wasu ’yan uwa da suka yi irin wannan yunƙurin ba su iya ganinsa ba.

Lauyoyin, a cewar majiyar, sun yi yunkurin ganin Tukur Mamu ne inda suka nemi belin sa a karshen mako musamman a ranar Juma’a ba tare da wani sakamako mai kyau ba.

Advertisement

Sai dai an tattaro cewa, mai yiwuwa ne a gurfanar da Mamu a gaban kotu ranar Litinin tare da ‘ya’yansa biyu da surukinsa, Abdullahi Mashi.

JARIDAR ALKIBLAH ta rawaito cewa Jami’an DSS a ranar Alhamis 8 ga watan Satumba, 2022 da misalin karfe 12:30 na safe sun kai farmaki gidan Mamu da ofisoshinsa da ke Kaduna sun kwashe wayoyi, kwamfutocin tafi da gidanka, kudi da sauran kayayyaki masu daraja.

Advertisement

Hukumar ta DSS ta ce ta gano wasu abubuwa da suka hada da makudan kudade iri daban-daban da kuma kayan sojoji a yayin samamen.

Sai dai hukumar gudanarwar jaridar Desert Herald a jerin jawabanta ta ce hukumar ta DSS ba ta gano wasu abubuwa da suka dame su ba a samamen, inda ta ce jami’an tsaro na karkatar da al’amura da kuma neman hanyar da za a yi wa Mamu igiya.

Advertisement

Ya kara da cewa babu wata doka da aka sani da ta haramta ajiye kudi a gidan musamman adadin kudin da aka samu a gidan da ofishin Tukur Mamu.

Sanarwar ta kuma ce, “Kayan da aka samu a gidansa kayan aikin soja ne na dansa wanda ya kammala karatunsa a makarantar horas da sojoji ta Najeriya

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending