Connect with us

News

RMAFC na shirin yi wa Buhari, Ahmad Lawan,Gwamnoni da sauran su ƙarin albashi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar tattara kudaden shiga da kasafi (RMAFC) ta bayyana shirin yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa, Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), gwamnonin jihohi, da dai sauransu ƙarin albashi.

Advertisement

Sanarwar da RMAFC ta fitar ta ce Shugaban Hukumar, Mohammed Bello Shehu ne ya sanar da shirin a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Shugaban Kungiyar Gwamnonin Na PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato a ofishinsa da ke Abuja.

DA ƊUMI-ƊUMI: CBN zai sauya launin takardar kuɗi a Disamba

Advertisement

Mohammed Bello ya bayyana cewa sakin layi na 32 (D) na sashi na 1 zuwa jadawalin na uku na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ya baiwa hukumar ikon kayyade albashin da ya dace da masu rike da mukaman siyasa, ma’aikata da ɓangaren shari’a a kasar.

Ya shaida wa Tambuwal cewa karo na karshe da aka yi gyaran albashin wadannan nau’o’in ‘yan Najeriya “an yi shi ne a shekarar 2008 wanda hakan ya sa har lokacin sake yin gyaran ya kure,”

Advertisement

A zantawarsa da jaridar The Nation, shugaban na RMAFC ya koka da abin da ya bayyana a matsayin rashin biyan albashin ma’aikatan gwamnati da na siyasa da na shari’a wanda hakan na haifar da cin hanci da rashawa.

A cewarsa: “Albashin ‘yan majalisar ya ma fi muni amma saboda suna da’awar cewa suna da ‘yancin cin gashin kansu sai suka hada dukkan alawus-alawus waje ɗaya.

Advertisement

“Akwai bukatar wannan bibiya. Na taba ganin alkalin da ke karbar Naira 150,000 duk wata. Wato alkali, wanda ya yanke hukunci. Ku je ku tambaya, sai kun yi al’ajabi. A kwai su a ko’ina cikin Najeriya, ba su da gidaje, ba su da motoci suna cikin mawuyacin yanayi na aiki,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending