News
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kalli atisayen makaman nukiliya da dakarun da ke kula da makaman nukiliyar kasar suka gudanar,
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
A daidai lokacin da yake ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen yamma kan mamayar da kasarsa ke yi wa Ukraine.
Fadar gwamnatin kasar ta ce an harba makaman nukiliyar masu yawa a yankin gabashin kasar.
An sanar wa Amurka game da atisayen, karkashin yarjejeniyar fara atisayen makamai ta duniya.
An gudanar da atisayen ne a daidai lokacin da Rasha ke ikirarin cewa Ukraine na shirin amfani da bom mai dauke da tarin sinadarai masu lahani, zargin da kasashen yamma da dama suka musanta.
Ukraine ta yi gargadin cewa ikirarin da Rashar ta yi, alama ce da ke nuna cewa Rasha na shirin kai irin wannan hari cikin kasarta.
Advertisements
